Hakikanin gaskiya mutane da dama sun yi wa yunkurin sulhu da masu garkuwa da mutane gurguwar fahimta.
Wannan kuwa ya faru ne saboda fahimtar da ta yawaita ga mutane cewa ba a yin sulhu da dan ta'adda saboda ba tawaye ba ne akan wata cutarwa da aka yi wa wani bangare na mutane.
Wannan fahimta daidai ce, to sai dai ba ta yi daidai da halin matsalar tsaron Zamfara ba musamman saboda wani salo da matsalar tsaron Zamfara ta dauka.
A halin yanzu matsalar tsaron ta dauki salon rikicin kabilanci saboda assasa kungiyar sa-kai ta zalla Hausawa da gwamnatin da ta shude ta yi inda a cikin su aka samu bara-gurbi da su ke kama da kuma yanka Fulani har a cikin kasuwa ba tare da bincike ba. Hasali ma an samu wadanda ke kama Fulani maza da mata wadanda ko dai suna zargin su ko kuwa 'yan uwa ko matan masu garkuwa da mutane ne, sai su su tsare su kamar yadda su ma masu garkuwa da mutane ke kama Hausawa.
Dalilin haka aka samu wani yanayi musamman a yankin Dansadau, Fulani su kama Hausawa, su kuwa 'yan Sa-kai su kama matan su ko 'ya'yan su ko duk wani Fulani da suka rutsa da shi. Wannan yanayi shi ya wajabtar da yin sulhu kamar yadda Mai girma Gwamna (Dr) Bello Matawalle ya jagoranta saboda fahimtar cewa ba a yakin zalunci da zalunci.
Nasarar da ake samu yanzu ta fara ne tun ranar da aka rarrashi 'yan Sa-kai a yankin Dansadau suka saki wasu Fulani 25 da su ke tsare da su wadanda su ka hada da mata da kananan yara.
Akasari an gano da yawa daga cikin masu kisa da garkuwa da mutane sun hadu da wani rashin adalci da cutarwa. Misali, akwai labari mai tushe na wani mutum da an tabbatar da kyawun halin sa wanda ya hau babur ya tafi wani kauye wajen abokanan sa. Yana kan dawowa garin su mashin din sa ya lalace kan hanya. A daidai wannan lokacin ashe barayi sun yi dirar mikiya kauyen su, sun kashe mutane, sun sace dukiya mai tarin yawa. Sai 'yan-Sa-kai na yankin su suka zargi da wannan mutumin aka kitsa harin saboda ba ya gari a lokacin saboda haka suka dira gidan su, su kashe mahaifiyar sa, 'ya'yan sa da matar sa. Daga ranar zuciyar mutumin ta kekashe ya shiga dabar barayi da zummar sai ya rama kisan iyalin sa akan 'yan-sa-kai.
Wannan yana nuna cewa duk da aikin 'yan-sa-kai yana da matukar mahimmanci amma kuma wuce gona da iri da wasun su ke yi na haddasa samun sabon zubi na 'yan ta'adda.
Allah Ya kawo mana zaman lafiya a Zamfara da Najeriya baki daya.
Ibrahim Bello Zauma
SSA NEW MEDIA
11/7/2019
No comments:
Post a Comment